Zak 9:6-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Tattarmuka za su zauna a Ashdod,Zan kuma sa alfarmar Filistiya ta ƙare.

7. Zan kawar da jininsu daga bakinsu,Da kuma haramtattun abubuwa daga haƙoransu.Sauransu za su zama jama'ar Allahnmu,Za su zama kamar sarki cikin Yahuza.Mutanen Ekron za su zama kamar Yebusiyawa.

8. Zan kafa sansani kewaye da Haikalina saboda maƙiya,Don masu kai da kawowa.Ba wani azzalumi da zai ci su da yaƙi,Gama yanzu ni kaina na gani.”

Zak 9