Zak 10:9-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ko da yake na watsar da su cikin al'ummai,Duk da haka za su riƙa tunawa da ni daga ƙasashe masu nisa.Su da 'ya'yansu za su rayu, su komo.

10. Zan dawo da su gida daga ƙasar Masar,In tattaro su daga Assuriya,Zan kawo su a ƙasar Gileyad da ta Lebanon,Har su cika, ba sauran wuri.

11. Za su bi ta cikin tekun wahala,Zan kwantar da raƙuman teku,Kogin Nilu zai ƙafe duk da zurfinsa,Za a ƙasƙantar da Assuriya,Sandan sarautar Masar zai rabu da ita.

12. Zan ƙarfafa su,Za su yi tafiya da sunansa,Ni Ubangiji na faɗa.”

Zak 10