Yak 5:13-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. In waninku yana shan wuya, to, sai ya yi addu'a, in kuma waninku yana murna, to, sai ya yi waƙar yabon Allah.

14. In waninku yana rashin lafiya, to, sai ya kira dattawan ikkilisiya su yi masa addu'a, suna shafa masa mai da sunan Ubangiji.

15. Addu'ar bangaskiya kuwa, za ta warkar da marar lafiya Ubangiji kuma zai tashe shi, in ma ya yi zunubi, za a gafarta masa.

16. Saboda haka, sai ku riƙa bayyana wa juna laifofinku, kuna yi wa juna addu'a, don a warkar da ku. Addu'ar mai adalci tana da ƙarfin aiki ƙwarai da gaske.

17. Iliya ɗan adam ne kamarmu, amma da ya nace da addu'a kada a yi ruwa, sai da aka shekara uku da wata shida ba a yi ruwa a ƙasar ba.

Yak 5