Yak 1:26-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. In wani yana zaton shi mai addini ne, amma bai kame bakinsa ba, sai dai ya yaudari kansa, to, addinin mutumin nan na banza ne.

27. Addini sahihi kuma marar aibu a gaban Allah Ubanmu, shi ne a kula da gwauraye mata, da marayu a cikin ƙuntatarsu, a kuma a keɓe kai marar aibi daga duniya.

Yak 1