5. Sai aka ji wata murya daga kursiyin, tana cewa,“Ku yabi Allahnmu, ya ku bayinsa,Ku da kuke jin tsoronsa, yaro da babba.”
6. Sai na ji kamar wata sowar ƙasaitaccen taro, kamar ƙugin ruwa mai gudu, kamar aradu mai ƙara, suna cewa,“Halleluya! Gama Ubangiji AllahnmuMaɗaukaki shi ne yake mulki.
7. Mu yi ta murna da farin ciki matuƙa,Mu kuma ɗaukaka shi,Domin bikin Ɗan Ragon nan ya zo,Amaryarsa kuma ta kintsa.
8. An yardar mata ta sa tufafin lallausan lilinmai ɗaukar ido, mai tsabta.”Lallausan lilin ɗin nan, shi ne aikin adalci na tsarkaka.