3. Mamanki kamar bareyi biyu ne, wato tagwayen barewa ne.
4. Wuyanki kamar hasumiyar hauren giwa ne.Idonki kamar tafki ne cikin birnin Heshbon,Kusa da ƙofar Bat-rabbim.Hancinki kyakkyawa ne kamar hasumiyar Lebanon ta tsaron Dimashƙu.
5. Kin ɗaga kanki sama kamar Dutsen Karmel.Kitsattsen gashin kanki kamar shunayya mafi kyau ne,Yakan kama hankalin sarki.
6. Ke kyakkyawa ce ƙaunatacciyata,Kina sa ni jin daɗi a rai.
7. Kina da kyan gani kamar itacen dabino,Mamanki kamar nonnan dabino.