1. Ƙafafunki suna da kyau da takalmi,Ke mafificiyar budurwa!Tsarin cinyoyinki kamar aikin gwanin sassaƙa ne.
2. Cibinki kamar finjali ne, wanda bai taɓa rasa gaurayayyen ruwan inabi a ciki ba.Kwankwasonki kamar damin alkama ne a tsakiyar bi-rana.
3. Mamanki kamar bareyi biyu ne, wato tagwayen barewa ne.