W. W. 6:3-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Ƙaunataccena nawa ne, ni kuma tasa ce,Yana kiwon garkensa a cikin bi-rana.

4. Ƙaunatacciyata, kina kyakkyawa kamar Urushalima,Kyakkyawa kuma kamar birnin Tirza,Kina da shiga rai kamar ɗaya daga cikin biranen nan.

5. Ki daina dubana gama idanunki suna rinjayata,Gashinki yana zarya kamar garken awakiDa yake gangarowa daga tuddan Gileyad.

6. Haƙoranki farare fat kamar tunkiyar da aka yi mata sausayaAka yi mata wanka nan da nan.Ba giɓi, suna nan shar.An jera su tantsai.

7. Kumatunki suna haske bayan lulluɓi.

W. W. 6