W. W. 4:4-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Wuyanki kamar hasumiyar Dawuda yake, kewayayye sumul sumul,Inda aka rataye garkuwoyi dubu na jarumawa.

5. Mamanki kamar bareyi biyu ne,Wato tagwayen barewa, suna kiwo cikin furen bi-rana.

6. Har iskar safiya ta huro,Duhu kuma ya kawu,Zan zauna a kan tudun mur,Wato tudun kayan ƙanshi.

7. Ke kyakkyawa ce ƙaunatacciyata,Ba wanda zai kushe ki!

W. W. 4