Rom 7:14-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Mun dai san Shari'a aba ce ta ruhu, ni kuwa mai halin mutuntaka ne, bautar zunubi kawai nake yi.

15. Ban ma fahimci abin da nake yi ba. Don ba abin da nake niyya yi, ba shi nake aikatawa ba, abin da nake ƙi, shi nake yi.

16. To, idan abin da ba na niyya, shi nake yi, na yarda ke nan Shari'a aba ce mai kyau.

17. Ashe kuwa, ba ni nake yinsa ba ke nan, zunubin da ya zaune mini ne.

18. Don na sani ba wani abin kirki da ya zaune mini, wato a jikina. Niyyar yin abin da yake daidai kam, ina da ita, sai dai ikon zartarwar ne babu.

19. Nagarin abin da nake niyya yi kuwa, ba shi nake yi ba, sai dai mugun abin da ba na niyya, shi nake aikatawa.

Rom 7