19. Amma sa'ad da Sanballat Bahorone, da Tobiya Ba'ammone, bawa, da Geshem Balarabe, suka ji labari, sai suka yi mana ba'a, suka raina mu, suka ce, “Me kuke yi? Kuna yi wa sarki tayarwa ne?”
20. Ni kuwa sai na amsa musu, na ce, “Allah na Sama zai ba mu nasara, saboda haka mu mutanensa za mu tashe, mu kama gini, amma ba ruwanku, ba hakkinku, ba ku da wani abin tunawa a Urushalima.”