11. Yanzu al'ummai sun taru sunagāba da ke, suna cewa,“Bari a ƙazantar da ita,Bari mu zura mata ido.”
12. Amma ba su san nufin Ubangiji ba,Ba su gane shirinsa ba,Gama ya tara su ne kamardammunan da za a kaimasussuka.
13. “Ya Sihiyona, ki tashi, ki tattaka!Gama zan mai da ƙahonki ƙarfe,kofatanki kuwa tagulla,Za ki ragargaje al'ummai da yawa.”Za ki ba Ubangijin dukan duniyadukiyarsu da suka tara ta hanyarzamba,Wadatarsu kuma ga Ubangijin dukanduniya.