Mat 25:38-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

38. A yaushe kuma muka gan ka baƙo muka sauke ka, ko kuwa huntu muka tufasar da kai?

39. Ko kuma a yaushe muka gan ka da rashin lafiya, ko a kurkuku muka kula da kai?’

40. Sai Sarkin zai amsa musu ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, tun da yake kun yi wa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan'uwana mafi ƙanƙanta, ai, ni kuka yi wa.’

Mat 25