Mat 16:24-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk mai son bina, sai ya ƙi kansa, ya ɗauki gicciyensa, ya bi ni.

25. Duk mai son tattalin ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi.

26. Me mutum ya amfana in ya sami duniya duka a bakin ransa? Me kuma mutum zai iya bayarwa ya fanshi ransa?

Mat 16