Mak 5:15-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Farin cikinmu ya ƙare,Raye-rayenmu sun zama makoki.

16. Rawani ya fāɗi daga kanmu,Tamu tu ƙare, gama mun yi zunubi!

17. Saboda wannan zuciyarmu ta ɓaci,Idanunmu kuma suka duhunta.

18. Gama Dutsen Sihiyona ya zama kufai,Wurin yawon diloli.

Mak 5