M. Sh 5:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Musa ya kirawo Isra'ilawa duka, ya ce musu, “Ya ku Isra'ilawa, ku ji dokoki da farillai waɗanda nake muku shelarsu a yau! Sai ku koye su, ku aikata su sosai.

2. Ubangiji Allahnmu ya yi alkawari da mu a Horeb.

3. Ba da kakanninmu ne Ubangiji ya yi wannan alkawari ba, amma da mu ne, mu duka waɗanda suke da rai a yau.

M. Sh 5