Luk 19:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yesu ya shiga Yariko. Yana ratsa garin,

2. sai wani mutum mai suna Zakka, babba ne a cikin masu karɓar haraji, mai arziki ne kuma,

3. ya nemi ganin ko wane ne Yesu, amma ya kasa ganinsa saboda taro, don shi gajere ne.

4. Sai ya yi gaba a guje, ya hau wani durumi don ya gan shi, don Yesu ta nan zai bi.

Luk 19