5. Mika kuwa yana da ɗakin gumaka. Ya yi gumaka, da falmaransu, da kan gida. Ya keɓe ɗaya daga cikin 'ya'yansa maza domin ya zama firist nasa.
6. A wannan lokaci ba sarki a Isra'ila, kowa yana ta yin yadda ya ga dama.
7. Akwai wani saurayi Balawen da yake zama a Baitalami ta Yahudiya.
8. Saurayin kuwa ya yi ƙaura daga Baitalami. Sa'ad da yake tafiya sai ya iso gidan Mika, a ƙasar tudu ta Ifraimu.
9. Mika ya tambaye shi, “Daga ina ka zo?”Ya ce, “Ni Balawe ne na Baitalami ta Yahudiya, ina neman wurin da zan zauna.”