13. Wannan ita ce ka'idar zama keɓaɓɓe a ranar da keɓewarsa ta cika. Za a kai shi ƙofar alfarwa ta sujada,
14. ya miƙa wa Ubangiji hadayarsa ta ɗan rago bana ɗaya mara lahani don yin hadaya ta ƙonawa, da 'yar tunkiya bana ɗaya marar lahani ta yin hadaya don zunubi, da rago marar lahani don yin hadaya ta salama,
15. da kwandon abinci marar yisti da aka yi da lallausan gari kwaɓaɓɓe da mai, da ƙosai wanda aka yayyafa masa mai, da hadaya ta gari, da hadayu na sha.
16. Sai firist ɗin ya kai su gaban Ubangiji, ya miƙa hadaya don zunubi, da hadaya ta ƙonawa.
17. Ya kuma miƙa rago don hadaya ta salama ga Ubangiji tare da kwandon abinci, da ƙosai. Firist ɗin kuma zai miƙa hadaya ta gari, da hadaya ta sha.
18. Sai kuma keɓaɓɓen ya aske sumarsa a ƙofar alfarwa ta sujada, sa'an nan ya kwashe sumar, ya zuba cikin wutar da take ƙarƙashin hadaya ta salama.
19. Firist ɗin zai ɗauki dafaffiyar kafaɗar ragon, da malmala guda marar yisti daga cikin kwando, da ƙosai guda, ya sa su a tafin hannun keɓaɓɓen bayan da keɓaɓɓen ya riga ya aske sumarsa.