L. Kid 30:3-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Idan kuma mace ta yi wa'adi ga Ubangiji, ta kuma ɗaure kanta da rantsuwa tun tana yarinya a gidan mahaifinta,

4. idan mahaifinta ya ji wa'adinta da rantsuwarta wadda ta ɗaure kanta da su, bai ce mata kome ba, to, sai wa'adinta da rantsuwarta su tabbata.

5. Amma idan mahaifinta ya ji, ya nuna rashin yarda, to, wa'adinta da rantsuwarta ba za su tsaya ba, Ubangiji kuwa zai gafarce ta domin mahaifinta bai yardar mata ba.

L. Kid 30