14. Ba zan iya ɗaukar nawayar mutanen nan ni kaɗai ba, gama nauyin ya fi ƙarfina.
15. Idan haka za ka yi da ni, ina roƙonka ka kashe ni, idan na sami tagomashi a gare ka, don kada in rayu in ga wannan baƙin ciki.”
16. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Tattaro mini mutum saba'in daga cikin dattawan Isra'ila waɗanda aka sani su ne dattawa da shugabannin jama'ar, ka kawo su a alfarwa ta sujada, ka sa su tsaya tare da kai.
17. Ni kuwa zan sauko, in yi magana da kai a can. Zan ɗiba daga cikin ruhun da yake cikinka, in ba su. Su kuma za su ɗauki nawayar jama'ar tare da kai, domin kada ka ɗauki nawayar kai kaɗai.
18. Ka ce wa jama'ar, su tsarkake kansu don gobe, za su ci nama, gama Ubangiji ya ji gunagunin da suka yi, da suka ce, ‘Wa zai ba mu nama mu ci? Ai, zama cikin Masar ya fi mana.’ Domin haka Ubangiji zai ba su nama, za su kuwa ci.