L. Fir 25:13-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Ubangiji ya ce, “A wannan shekara ta hamsin ta murna kowa zai koma mahallinsa.

14. In ka sayar, ko ka sayi gona a wurin ɗan'uwanka, Ba'isra'ile, kada ku cuci juna.

15. Idan za ka yi sayayya a wurin maƙwabcinka, sai ka lura da yawan shekarun da za ka mora kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo.

L. Fir 25