20. A sa'ad da ya gama yin kafara don Wuri Mai Tsarki, da alfarwa ta sujada, da bagaden, sai ya miƙa bunsuru ɗin mai rai.
21. Haruna zai ɗibiya hannuwansa duka biyu a kan kan bunsurun mai rai, ya hurta muguntar Isra'ilawa duka a bisa bunsurun, da dukan laifofinsu, da dukan zunubansu. Zai ɗibiya su a kan kan bunsurun, ya kora shi cikin jeji ta hannun wanda aka shirya zai kora shi.
22. Bunsurun zai ɗauki muguntarsu duka a kansa zuwa jeji. Mutumin kuwa zai sake shi can a jeji.
23. Sa'an nan Haruna zai shiga alfarwa ta sujada, ya tuɓe tufafinsa na lilin waɗanda ya sa sa'ad da ya shiga Wuri Mafi Tsarki, ya ajiye su a nan.