5. Don ko da yake a jiki ba na nan, ai, ruhuna yana nan tare da ku, ina kuwa farin cikin ganin kyakkyawan tsarinku, da dagewarku a kan bangaskiyarku ga Almasihu.
6. Da yake kun yi na'am da Almasihu Yesu Ubangiji, to, sai ku tsaya a gare shi,
7. kuna kafaffu, kuna ginuwa a cikinsa, kuna tsayawa da bangaskiya gaba gaba, daidai yadda aka koya muku, kuna gode wa Allah a koyaushe.
8. Ku lura fa, kada kowa ya ribace ku ta hanyar iliminsa na yaudarar wofi, bisa ga al'adar mutane kawai, wato, bisa ga al'adun duniyar nan, ba bisa ga koyarwar Almasihu ba.
9. Domin a cikinsa ne cikin jiki dukkan cikar Allahntaka take tabbata.
10. A gare shi ne aka kammala ku, wanda yake shi ne shugaban dukkan sarauta da iko.