Kol 1:21-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Ku kuma dā a rabe kuke da Allah, maƙiyansa a zuci, masu mugun aiki.

22. Amma a yanzu ya sulhunta ku ta hanyar jikinsa na mutuntaka, wato, ta wurin mutuwarsa, domin ya miƙa ku tsarkakakku, marasa aibu, marasa abin zargi kuma a gabansa.

23. Sai dai fa ku nace wa bangaskiya, zaunannu, kafaffu, ba tare da wata ƙaura daga begen nan na bishara wadda kuka ji ba, wadda aka yi wa dukkan talikan da suke a duniya, wadda kuma ni Bulus na zama mai hidimarta.

24. To, a yanzu ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, a jikina kuma ina cikasa abin da ya saura ga wahalar Almasihu, da aka aza mini saboda jikinsa, wato Ikilisiya,

25. wadda na zama mai hidimarta bisa ga aikin nan da Allah ya ba ni amana saboda ku, domin in sanar da Maganar Allah sosai,

26. wato, asirin nan da yake a ɓoye tun zamanai masu yawa, amma a yanzu an bayyana shi ga tsarkakansa.

Kol 1