1. Sa'ad da dukan sarakunan Amoriyawa waɗanda suke wannan hayi, wato yamma da Urdun, da dukan sarakunan Kan'aniyawa da suke bakin teku, suka ji yadda Ubangiji ya sa ruwan Urdun ya ƙafe don Isra'ilawa, har suka haye, sai zukatansu suka narke, har ba wanda yake da sauran kurwa a cikinsu saboda tsoron Isra'ilawa.
2. A lokacin kuwa Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “Ka yi wuƙaƙe na duwatsu, ka yi wa mazajen Isra'ila kaciya.”
3. Sai Joshuwa ya yi wuƙaƙe na duwatsu, ya yi wa mutanen kaciya a Gibeyat-ha'aralot, wato dutsen kaciya.
4-5. Dalilin da ya sa Joshuwa ya yi musu kaciya ke nan, domin dukan waɗanda aka haifa a hanya cikin jeji bayan fitowarsu daga Masar, ba a yi musu kaciya ba. Dukan mazajen da suka fito daga Masar waɗanda suka isa yaƙi sun rasu cikin jeji a hanyarsu. Waɗannan kuwa an yi musu kaciya kafin fitowarsu.
10. Sa'ad da Isra'ilawa suke zaune a Gilgal, sai suka yi Idin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu ga watan, da maraice, a filayen Yariko.
11. A kashegarin idin, a wannan rana, sai suka ci daga cikin amfanin ƙasar, waina marar yisti da busasshiyar tsaba.
12. Kashegari bayan da suka ci amfanin ƙasar kuwa, mannar ta yanke, mutanen Isra'ila kuma ba su ƙara samunta ba. A wannan shekara suka fara cin amfanin ƙasar Kan'ana.
13. Lokacin da Joshuwa yake daura da Yariko, ya ta da idanunsa ya duba, sai ya ga mutum a tsaye a gabansa da takobinsa a zare a hannunsa. Joshuwa ya tafi wurinsa, ya ce masa, “Kana wajenmu ne, ko kuwa kana wajen abokan gābanmu?”
14. Sai mutumin ya ce, “A'a, gama na zo ne kamar sarkin yaƙin rundunar Ubangiji.”Sai Joshuwa ya sunkuyar da kansa, ya rusuna har ƙasa, ya yi sujada, ya ce masa, “Wace magana ce Ubangiji yake faɗa wa bawansa?”
15. Sarkin yaƙin rundunar Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “Cire takalmanka da suke a ƙafafunka, gama wurin da kake tsaye tsattsarka ne.” Haka kuwa Joshuwa ya yi.