Josh 4:16-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. “Ka umarci firistocin da suke ɗauke da akwatin shaida, su fito daga cikin Urdun.”

17. Sai Joshuwa ya umarci firistocin su fito daga cikin Urdun.

18. Da firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari na Ubangiji suka fito daga tsakiyar Urdun, suka taka sandararriyar ƙasa, sai ruwan Urdun ya malalo ya tumbatsa kamar dā.

Josh 4