7. domin kada ku yi cuɗanya da sauran al'umman da take zaune tare da ku, kada ku ambaci sunayen gumakansu, ko ku rantse da su, ko ku bauta musu, ko ku sunkuya musu.
8. Amma ku manne wa Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka yi har wa yau.
9. Gama Ubangiji ya kori manyan al'ummai ƙarfafa daga gabanku, har wa yau ba mutumin da ya isa ya yi hamayya da ku.
10. Mutuminku guda zai runtumi mutum dubu nasu, tun da yake Ubangiji Allahnku ne yake yaƙi dominku, kamar yadda ya alkawarta muku.
11. Ku kula da kanku sosai, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku.
12. Gama idan kun kauce, kun koma da baya, kun haɗa kai da sauran al'umman nan da take tare da ku, har kuka yi aurayya da juna,
13. to, sai ku tabbata Ubangiji Allahnku ba zai dinga korar al'umman nan daga gabanku ba, za su zama muku azargiya, da tarko, da bulala a kwiyaɓunku, da ƙayayuwa a idanunku. Da haka za ku ƙare sarai daga cikin kyakkyawar ƙasan nan da Ubangiji Allahnku ya ba ku.