14. Amma suka taurare, suka biye wa zuciyarsu, suka bi Ba'al, kamar yadda kakanninsu suka koya musu.
15. Domin haka, ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, zan ciyar da mutanen nan da abinci mai ɗaci, in shayar da su da ruwan dafi.
16. Zan watsa su cikin sauran al'umma waɗanda su da kakanninsu ba su san su ba, zan sa takobi ya bi su don in hallaka su.