14. Mutanen Urushalima sun ce,“Don me muke zaune kawai?Bari mu tattaru, mu tafi cikingaruruwa masu garu,Mu mutu a can,Gama Ubangiji Allahnmu yaƙaddara mana mutuwa,Ya ba mu ruwan dafi,Domin mun yi masa laifi.
15. Mun sa zuciya ga salama, amma balafiya,Mun sa zuciya ga lokacin samunwarkewa,Amma sai ga razana!
16. Daga Dan, an ji firjin dawakai.Dakan ƙasar ta girgiza sabodahaniniyar ingarmunsu.Sun zo su cinye ƙasar duk da abinda suke cikinta,Wato da birnin da mazaunacikinsa.”