Fit 6:28-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Wata rana Ubangiji ya yi magana da Musa a ƙasar Masar ya ce,

29. “Ni ne Ubangiji, sai ka faɗa wa Fir'auna, Sarkin Masar, dukan abin da na faɗa maka.”

30. Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ni mai nauyin baki ne, yaya Fir'auna zai kasa kunne gare ni?”

Fit 6