Fit 20:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Allah ya faɗi dukan waɗannan zantuttuka, ya ce,

2. “Ni ne Ubangiji Allahnka wanda ya fisshe ka daga ƙasar Masar, daga gidan bauta.

3. “Kada ka kasance da waɗansu alloli sai ni.

4. “Kada ka yi wa kanka wani gunki ko kuwa wata siffa ta wani abu a sama a bisa, ko a duniya a ƙasa, ko kuma a ruwa a ƙarƙarshin ƙasa.

Fit 20