Fit 17:7-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Sai aka sa wa wurin suna, “Masaha” da “Meriba”, saboda Isra'ilawa suka yi husuma, suka kuma jarraba Ubangiji suna cewa, “Ubangiji yana tare da mu, ko babu?”

8. Amalekawa suka zo su yi yaƙi da Isra'ilawa a Refidim.

9. Sai Musa ya ce wa Joshuwa, “Zaɓo mana mutane, ka fita ka yi yaƙi da Amalekawa gobe. Zan tsaya a bisa dutsen da sandan mu'ujiza a hannuna.”

Fit 17