22. Musa kuwa ya bi da Isra'ilawa daga Bahar Maliya, suka shiga jejin Sur. Suka yi tafiya kwana uku cikin jejin, ba su sami ruwa ba.
23. Sa'ad da suka zo Mara, sun kasa shan ruwan Mara saboda ɗacinsa, don haka aka sa masa suna Mara.
24. Sai mutanen suka yi wa Musa gunaguni suna cewa, “Me za mu sha?”
25. Musa ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya nuna masa wani itace. Sa'an nan Musa ya karyi itacen, ya jefa cikin ruwa, ruwan kuwa ya zama mai daɗi.A nan ne Ubangiji ya kafa musu dokoki da ka'idodi, a nan ne kuma ya gwada su.