1. Sarki Dariyus kuwa ya ba da umarni a bincike ɗakin littattafai na Babila, inda aka ajiye takardun shaida.
2. Sai aka sami takarda a Ekbatana, babban lardin Mediya. A cikin takardar aka iske rubutu don tunawa.
3. “A shekara ta fari ta sarautar sarki Sairus, sai ya ba da izini a sāke gina Haikalin Allah da yake a Urushalima, wurin da za a miƙa sadaka da hadayu na ƙonawa. Sai a aza harsashi da ƙarfi. Tsayinsa zai zama kamu sittin, fāɗinsa kuwa kamu sittin.
4. Za a jera manyan duwatsu jeri uku, da jeri ɗaya na katako, a kuma biya kuɗin aikin daga baitulmalin sarki.