Dan 8:13-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sai na ji wani mai tsarki yana magana, wani kuma mai tsarki ya tambayi wancan mai tsarki da ya yi magana, ya ce, “Sai yaushe za a tsai da abubuwan da suke a wahayin nan, wato hana yin hadayar ƙonawa ta yau da kullum, da zunubin da yake lalatarwa, da ba da wuri mai tsarki ga rundunar mutane don a tattake?”

14. Ya ce mini, “Sai an yi kwana dubu biyu da ɗari uku, sa'an nan za a mai da wuri mai tsarki daidai da yadda yake a dā.”

15. Sa'ad da ni Daniyel, na ga wahayin, ina so in gane, sai ga wani kamar mutum ya tsaya a gabana.

16. Na kuma ji muryar mutum a gāɓar Ulai ta ce, “Jibra'ilu, ka sa wannan mutum ya gane wahayin.”

17. Don haka sai ya zo kusa da inda nake tsaye. Da ya zo sai na firgita, na faɗi rubda ciki.Amma ya ce mini, “Ɗan mutum, wannan wahayi yana a kan lokaci na ƙarshe ne.”

Dan 8