Ayu 8:9-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Kwanakinmu 'yan kaɗan ne kawai,Ba mu san kome ba,Mu inuwa ne kawai a fuskar duniya.

10. Amma ka yarda masu hikima na zamanin dā su koya maka,Ka kasa kunne ga abin da za su faɗa.

11. “Iwa ba ta tsirowa inda ba ruwa,Ba a taɓa samunta a ko'ina ba sai a fadama.

12. In ruwan ta ƙafe, ita ce za ta fara bushewa,Tun tana ƙanƙana ba ta isa a yanke a yi amfani da ita ba.

13. Marasa tsoron Allah kamar iwan nan suke,Ba su da sa zuciya muddin sun rabu da Allah.

14. Suna dogara ga silin zare, murjin gizo-gizo.

15. Idan suka jingina ga saƙar gizo-gizo, za ta iya tokare su?Idan sun kama ta, za ta taimake su tsayawa?

Ayu 8