Ayu 36:3-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Zan tattaro ilimina daga nesa,In bayyana adalcin Mahaliccina.

4. Gaskiya nake faɗa ba ƙarya ba,Wanda yake da cikakken sani yana tare da kai.

5. “Ga shi kuwa, Allah Mai Girma, ba ya raina kowa,Shi mai girma ne, mai cikakkiyar basira.

6. Ba ya rayar da masu laifi,Amma yakan ba waɗanda ake tsananta wa halaliyarsu.

7. Yakan kiyaye waɗanda suke aikata gaskiya,Yakan kafa su har abada tare da sarakuna,A gadon sarauta, ya ɗaukaka su.

Ayu 36