Ayu 26:3-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Kai ne kake ba marar hikima shawara,Kai kake sanar da ilimi mai ma'ana a wadace!

4. Kana tsammani wane ne zai ji maganganunka duka?Wane ne ya iza ka ka yi irin wannan magana?

5. “Lahira tana rawa,Mazaunanta suna rawar jiki don tsoro.

6. Lahira tsirara take a gaban Allah,Haka kuma Halaka take a gaban Allah.

7. Allah ne ya shimfiɗa arewa a sarari kurum,Ya rataya duniya ba bisa kan kome ba.

8. Allah ne ya cika gizagizai masu duhu da ruwa,Girgijen kuwa bai kece ba.

Ayu 26