16. Da zan ci nasara a kan kowane abu,Da sai ka yi ta farautata kamar zaki,Kana aikata al'ajabai don ka cuce ni.
17. A koyaushe kakan karɓi shaida gāba da ni,Fushinka sai gaba gaba yake yi a kaina,Kakan yi mini farmaki a koyaushe.
18. “Ya Allah, me ya sa ka bari aka haife ni?Da ma na mutu tun kafin wani ya gan ni!
19. Da a ce daga cikin cikin mahaifiyata an wuce da ni zuwa kabariDa ya fi mini kyau bisa ga kasancewata.
20. Raina bai kusa ƙarewa ba? A bar ni kawai!Bari in ci moriyar lokacin da ya rage mini.
21. An jima kaɗan zan tafi, ba kuwa zan komo ba faufau,Zan tafi ƙasa mai duhu, inda ba haske,