Amos 5:24-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Sai ku sa adalci da nagarta su gudanoa yalwaceKamar kogin da ba ya ƙafewa.

25. “Ya ku, jama'ar Isra'ila, ai, a waɗannan shekaru arba'in da kuka yi cikin jeji kuka kawo mini sadaka da hadayu,

26. duk da haka, kuka ɗauki siffofin gumakanku na taurari, wato Sakkut da Kaiwan, waɗanda kuka yi wa kanku.

Amos 5