A.m. 11:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. To, manzanni da 'yan'uwan da suke a ƙasar Yahudiya suka ji, cewa al'ummai ma sun yi na'am da Maganar Allah.

2. Da Bitrus ya zo Urushalima, 'yan ɗariƙar masu kaciyar nan suka yi masa sūka,

3. suka ce, “Ga shi, ka shiga wurin marasa kaciya, har ka ci abinci tare da su!”

A.m. 11