A.m. 1:23-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Sai suka nuna mutum biyu, Yusufu mai suna Barsaba, wanda aka yi wa laƙabi da Yustus, da kuma Matiyas.

24. Sai suka yi addu'a, suka ce, “Ya Ubangiji, masanin zuciyar kowa, a cikin waɗannan mutum biyu ka nuna wanda ka zaɓa,

25. yă karɓi matsayi cikin aikin nan da manzancin nan da Yahuza ya bauɗe wa, don yă cike gurbinsa.”

A.m. 1