2 Tas 3:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Daga ƙarshe kuma 'yan'uwa, ku yi mana addu'a, Maganar Ubangiji ta yi saurin yaɗuwa, ta sami ɗaukaka, kamar yadda ta samu a gare ku,

2. a kuma cece mu daga fanɗararrun mutane, mugaye. Don ba duka ne suke da bangaskiya ba.

3. Amma Ubangiji mai alkawari ne, zai kuwa kafa ku, ya tsare ku daga Mugun nan.

2 Tas 3