7. Sa'an nan firistoci suka shigar da akwatin alkawari na Ubangiji a wurinsa, wato a Wuri Mafi Tsarki na cikin Haikalin, a ƙarƙashin fikafikan kerubobi.
8. Gama kerubobin sun miƙe fikafikansu bisa a daidai wurin da akwatin yake, wato kerubobin sun yi wa akwatin da sandunansa kamar rumfa ke nan.
9. Sandunan akwatin dogaye ne ƙwarai, har ana ganin kawunansu a gaban Wuri Mafi Tsarki na can ciki. Amma daga waje ba a iya ganinsu. Suna a wannan wuri har yau.
10. Ba kome cikin akwatin sai alluna biyu waɗanda Musa ya sa a ciki sa'ad da suke a Horeb. A Horeb ne Ubangiji ya ƙulla alkawarin da mutanen Isra'ila, sa'ad da suka fito daga Masar.
11. Firistocin suka fito daga Wuri Mai Tsarki na Haikalin Allah, gama dukan firistocin da suka hallara, sun tsarkake kansu ba tare da kula da bambancin matsayi ba.
12. Dukan Lawiyawa mawaƙa, wato su Asaf, da Heman, da Yedutun tare da 'ya'yansu maza da 'yan'uwansu, aka sa su su tsaya a gabashin bagade, suna sāye da lilin mai kyau, suna ta kaɗa kuge, da molaye da garayu, ga kuma firistoci ɗari da ashirin masu busa ƙaho tare da su.