8. Ya kuma yi tebur goma, ya ajiye a cikin Haikalin, biyar a dama, biyar kuma a hagu. Ya kuma yi kwanonin zinariya guda ɗari.
9. Sa'an nan ya yi wani shirayi domin firistoci, ya kuma yi wani babban shirayi, ya yi ƙofofi domin shirayun. Ya dalaye ƙyamaren ƙofofin da tagulla.
10. Ya girka kwatarniya a kusurwar kudu maso gabas daura da Haikalin.
17. Sarki ya yi zubinsu a filin Urdun tsakanin Sukkot da Zaretan a wuri mai yumɓu.