8. Sauran ayyukan Yehoyakim da irin abubuwan da ya yi na banƙyama, da irin laifofinsa, suna nan, an rubuta su a littafin sarakunan Isra'ila da na Yahuza. Ɗansa Yekoniya kuwa ya gāji gadon sarautarsa.
9. Yekoniya yana da shekara takwas sa'ad da ya ci sarauta, ya yi sarauta a Urushalima wata uku da kwana goma. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji.
10. Da bazara sai sarki Nebukadnezzar ya aika aka kawo shi Babila tare da kayayyaki masu daraja na Haikalin Ubangiji. Ya kuma naɗa Zadakiya ɗan'uwan Yekoniya ya zama Sarkin Yahuza da Urushalima.
11. Zadakiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa'ad da ya ci sarauta, ya yi shekara goma sha ɗaya yana sarautar Urushalima.
12. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnsa. Bai nuna ladabi a gaban annabi Irmiya ba, wanda ya faɗa masa abin da Ubangiji ya ce.