2 Tar 3:10-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ya sassaƙa siffofin kerubobi biyu na itace, a Wuri Mafi Tsarki, ya shafe su da Zinariya.

11. Tsawon fikafikan kerubobin duka kamu ashirin ne, fiffike ɗaya, kamu biyar, ya taɓo bangon ɗakin, ɗaya fiffiken kuma wanda shi ma kamu biyar ne, ya taɓo fiffiken kerub ɗaya ɗin.

12. Guda kerub ɗin kuma, fiffikensa guda ya taɓo bangon ɗakin, ɗaya fiffiken shi ma ya taɓo fiffiken kerub na farko.

13. Tsawon fikafikan kerubobin ya kai kamu ashirin. Su kerubobin a tsaye suke, suna fuskantar babban ɗakin.

14. Sai ya yi labule mai launin shuɗi, da shunayya, da garura, da lilin mai kyau, sa'an nan ya zana siffofin kerubobin a jikin labulen.

2 Tar 3