26. Waɗannan su ne waɗanda suka yi masa maƙarƙashiyar, Yozakar ɗan Shimeyat wata Ba'ammoniya, da Yehozabad ɗan Shimrit wata mutuniyar Mowab.
27. Labarin 'ya'yansa maza da annabcin da aka kawo a kansa da labarin sāke ginin Haikalin Allah, an rubuta su a sharhin littafin sarakunan. Sai Amaziya ɗan Yowash ya gāji gadon sarautarsa.