2 Tar 23:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A shekara ta bakwai sai Yehoyada ya yi ƙarfin hali, ya haɗa kansa da shugabanni na ɗari ɗari, wato Azariya ɗan Yeroham, da Isma'ilu ɗan Yehohanan, da Azariya ɗan Obed, da Ma'aseya ɗan Adaya, da kuma Elishafat ɗan Zikri.

2. Sai suka shiga ko'ina cikin Yahuza, suka tattaro Lawiyawa daga dukan biranen Yahuza, da shugabannin gidajen kakannin Isra'ila, suka kuwa zo Urushalima.

2 Tar 23